Dan kasuwa ya kone kurmus lokacin da yake kwato kaya daga shagonsa yayin da gobara ta tashi a kasuwar Zamfara


Hukumar kashe gobara ta bayyana cewa, wani dan kasuwa ya kone kurmus a lokacin da yake kwato dukiyarsa daga shagonsa da ke babbar kasuwar Gusau a jihar Zamfara
. Wata mummunar gobara ta barke a kasuwar lamarin da ya yi sanadiyar lalata shaguna da dama. Gobarar wacce ta tashi da misalin karfe 9 na daren ranar Talata, ta kone bangaren kayan daki na babbar kasuwar jihar. Daraktan hukumar kashe gobara ta Zamfara Abdullahi Dauran, ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na Najeriya a Gusau afkuwar lamarin. "Mun samu rahoton barkewar gobarar kuma muka tura mutanenmu wurin," in ji shi. “Mun samu nasarar shawo kan gobarar, amma mutum daya ya rasa ransa a lokacin da yake kokarin kwashe kadarorinsa daga shagonsa. Dauran ya kara da cewa, "Muna gudanar da bincike don gano musabbabin faruwar lamarin da kuma gano hakikanin barnar da Gobara ta yi."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN