Bayan cire tallafin man fetur, Ministan Tinubu ya bukaci cire na wutar lantarki, ya fadi dalilai



Ministan Makamashi a Najeriya, Adebayo Adelabu ya nuna damuwa kan matsalar wutar lantarki a kasar.

Adelabu ya danganta matsalar da yawan basukan tallafi inda ya ce dole a sauya salo idan har gwamnati ba za ta iya biyan

Ya ce dole a cire tallafin wutar gaba daya idan har ba za a iya biyan kudaden tallafi ba da ‘yan kasuwar ke bi. Legit Hausa ya wallafa.

Ministan ya bayyana haka ne a jiya Laraba 31 ga watan Janairu yayin kai ziyara kamfanin wuta na Olorunsogo a jihar Ogun, cewar Arise News.

Ya ce:

Muna rokon Gwamnatin Tarayya idan har akwai alkawarin tallafi, to dole a biya su gaba daya.

“Idan har gwamnatinmu ba ta shirya biyan kudaden tallafin ba to ya zama dole sai an cire tallafi a bangaren wutar lantarki.

“Da zarar su na bin bashi, to ba za su iya biyan kudaden siyan gas ba wanda hakan zai kara jawo matsala a samar da wutar a kasar.”

Adelabu ya ce ya yi zama da Ministan Kudade da kuma na ma’aikatar kasafi da tsare-tsare don neman hanyar biyan kudaden, cewar Leadership.

Ya kara da cewa, a duk fadin Nahiyar Afirka ta Yamma, Najeriya ce ke biyan mafi karancin kudin wutar lantarki.

Ministan ya ce kasashe kamar su Ghana da Nijar da Ivory Coast su na biyan kusan ninkin kudaden da ‘yan Najeriya ke biya.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN