Yan bindiga sanye da hijabi sun afka wa ofishin yan sanda a Katsina

 

Rahotanni sun bayyana cewa wasu ‘yan bindiga sanye da hijabi sun kai hari a ofishin ‘yan sanda da ke kauyen Saki Jiki da ke karamar hukumar Batsari a jihar Katsina, inda suka kashe jami’in dan sanda guda.


 Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, Abubakar Aliyu, wanda ya tabbatar wa manema labarai hakan a ranar Juma’a, 19 ga watan Janairu, 2024, ya ce wani dan sanda ya samu rauni a harin.


 Ya ce lamarin ya faru ne da karfe 8 na daren ranar Alhamis, 18 ga watan Janairu.


 “Jiya (Alhamis) da misalin karfe 8:00 na dare wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sanye da hijabi, sun kai wa jami’an hari a ofishinsu dake kauyen Saki Jiki na karamar hukumar Batsari,” in ji PPRO.


 “Jami’an sun mayar da martani cikin jarumtaka tare da samun nasarar dakile harin, amma jami’i daya ya rasa ransa, wani kuma ya samu rauni sakamakon harin.


 "Za a sanar da Ζ™arin ci gaba don Allah."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN