Yadda yan iska suka sace gawa daga asibiti bayan sun farmaki likitoci har ma'aikatan jinya


Wasu mutane a ranar Litinin, 15 ga watan Janairu, 2024, sun kai farmaki asibitin koyarwa na jami’ar jihar Ekiti (EKSUTH), Ado-Ekiti, inda suka far wa likitoci da wasu jami’an lafiya dake bakin aiki kan mutuwar wani dan uwansu a asibitin koyarwa a sashen A&E. An tattaro cewa mutanen da suka kai farmaki asibitin koyarwa sun kuma lalata wasu kadarori kafin su tafi da wata gawa da ake zargin mahaifin daya daga cikin mutanen masu ta da zaune tsaye ne. An bayyana cewa mutumin da aka kawo sashin Hatsari da kulawar Gaggawa na asibitin ya rasu ne da sanyin safiyar ranar Litinin, kuma dan marigayin wanda daya ne daga cikin maharan ya zargi likitoci da ma’aikatan lafiya da ke bakin aiki da yin sakaci da rashin iya aiki kuma haka ya haddasa rasuwar mahaifinsa.


 Dan marigayin wanda ya fusata da lamarin, tare da wasu ma'aikatan NURTW ne suka kai wa likitoci da ma’aikatan lafiya hari, suka kore su suka tafi da gawar ba tare da biyan kudin magani ba.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN