Matashin ya gamu da tsautsayin inda mota ta murkushe shi jim kadan bayan kwace wayar don tsallaka titi. Legit Hausa ya wallafa.
Kakakin rundunar 'yan sanda a Kano, Haruna Abdullahi Kiyawa shi ya bayyana haka a shafinsa na Facebook.
Kiyawa ya ce lamarin ya faru ne a daren jiya Lahadi 14 ga watan Janairu a Zoo Road yayin da ya ke kokarin tserewa.
Ya ce matashin ya fito da makami don razana matar inda ya yi nasarar kwace wayar amma ya ci karo da motar inda ta kade shi.
Ya kara da cewa an kira jami'an 'yan sanda don daukar shi zuwa asibiti tare da ba shi kulawar gaggawa, cewar Leadership.
Daga bisani bayan daukar shi zuwa asibiti, Kiyawa ya ce kashin bayan matashin ya karye kuma kansa ya fashe.
Ya ce asibitin su na tunanin shigar da shi bangaren 'ICU' don ceto rayuwarsa cikin gaggawa.
Birnin Kano na fama da 'yan daba wadanda su ka kware wurin kwacen wayar mutane a wurare da dama na birnin.
From ISYAKU.COM