Mutum 7 yan gida daya sun mutu sakamakon gobara da ta tashi a Tudun Wada Bompai dake karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano.
Wani jami’in hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Alhaji Saminu Abdullah, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Litinin, 15 ga watan Janairu, 2024, ya ce uba da uwa da ‘ya’yansu biyar sun mutu a lamarin wanda ya faru a daren Lahadi, 14 ga watan Janairu.
“Mun samu kiran gaggawa a tashar kashe gobara ta Dakata daga wani Ibrahim Sani da misalin karfe 12:25 na dare cewa gobara ta tashi a wani gini da ke Tudun Wada Quarters,” inji shi.
"Da samun labarin, mun aika da motar kashe gobara zuwa wurin da misalin karfe 12:30 na dare,"
Ya ce, ‘yan kwana-kwana sun kwashe mutane bakwai da suka sume daga cikin dakuna biyu da suka kone, aka garzaya da su asibiti.
“Likitan ya tabbatar da mutuwar bakwai daga cikin su sakamakon hayakin da suka shaka,” inji shi, ya kuma kara da cewa bincike ya nuna cewa gobarar da ta tashi daga wutar lantarki, ta kare a lokacin da jami’an kashe gobara suka isa wurin.
From ISYAKU.COM