Innalillahi: Ƴan bindiga sun kai hari sanye da kakin sojoji, sun tafka mummunar ɓarna a jihar arewa


Miyagun 'yan bindiga sanye da kakin sojoji sun yi garkuwa da wasu mutanen kauye 31 a wani hari da suka kai kauyen Tashar Nagule, ƙaramar hukumar Batsari a jihar Katsina.

Wata majiya mai tushe a yankin ta bayyana cewa ‘yan bindiga da yawa sun kutsa kai cikin ƙauyen ba zato ba tsammani sanye da kayan sojoji a daren Lahadi. Legit Hausa ya wallafa.

Ya ce bayan gama tsara kansu, maharan sun tattara mazauna ƙauyen da suka ƙunshi mata da kananan yara, suka yi awon gaba da su, jaridar Leadership ta ruwaito.

Mutumin ya yi bayanin cewa da farko ƴan ta'addan sun kewaye kauyen kana daga bisani suka aiko wasu daga ciki suka shigo suka tafi da mutane kusan 31.

Ya ce:

"Muna zaune a ƙofar gida ni da abokaina wajen karfe 9:00 na daren kwatsam muka fara jin ƙarar harbe-harben bindiga. Mun tashi zamu gudu amma maharan suka daka mana tsawa.

"Suka gaya mana jami'an tsaro ne aka turo su tsare mu, sun san idan suka ce ƴan sanda ne ko sojoji aka turo mana zamu yarda da su, kuma abinda ya faru kenan."

Majiyar ta ƙara da cewa bisa haka yan ƙauyen suka fara taruwa a dandali ba tare da sanin waɗannan mutanen da ke sanye da rigar sojoji ba jami'an tsaro bane ƴan bindiga ne.

"Lokacin da ‘yan ta’addan suka zagaye mutanen garin, sai suka ce su bi su cikin dajin, a lokacin muka gane ba jami’an tsaro ba ne. Na faki ido na fice da gudu zuwa gida."

Ya ce zuwa yau Litinin, sun tantance mutane 31 da maharan suka yi awon gaba da su. Ƴan bindigan sun haɗa da wasu da suka gudu zuwa jeji don neman tsira.

Har yanzu rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ba ta fitar da sanarwa a hukumance ba dangane da sabon harin da aka kai, rahoton The News.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN