Daga ziyartar saurayi a gidansa, neman lalata yasa ta sheke shi


A cewar Vanguard, Sarah ta sirace ne daga gidan saurayinta, Joe Ibanga zuwa gidan marigayin a ranar 22 ga Disamba, 2023, inda lamarin ya faru, Vanguard ta ruwaito.

Sarah ta bayyana cewa ta hadu da Igbodike ne a 2017 lokacin da take zaune a Enugu kafin ta koma Fatakwal a watan Agustan 2023. Legit Hausa ya wallafa.

Ta ce marigayin yakan gayyace ta ta zo gidansa, wani lokacin kuma ya aika mata da kudin sufuri don ta zo su aikata abin da za su aikata.

A karshe dai ta ziyarce shi kuma ta yi lalata da shi a ranar 22 ga Disamba, 2023, bayan ya sake kira ya gayyace ta don zuwa wurinsa, Within Nigeria ta tattaro.

Da take ba da labarin yadda abin takaicin ya faru, ta ce:

“Da ya gama cin abinci, sai ya ce na masa tausa. Na bi abin da ya fadi amma daga baya na daina lokacin da ya bukaci jima'i daga gare ni. Na ce masa ba ni da kwanciyar hankali yin hakan.

“Kin amincewa da na yi ya bata masa rai. Ya ce in shirya in bar gidansa. Lokacin karfe 10 na dare. Na ki fita na tsaya na kalubalance shi. Mun yi cacar baki.”

Mai gidan da suke ciki da ’yan uwansa nan take suka ankara a lokacin da Sarah ta yi kokarin tserewa daga gidan bayan ta aikata laifin kashe abokin fajircinta.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN