Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar wa yan Najeriya cewa duk wanda aka kama da hannu a harin bama-baman da aka kai kauyen Kaduna zai ɗanɗana kuɗarsa.
Shugaba Tinubu ya ce duk wanda aka gano yana da hannu a harin bama-baman wanda ya yi ajalin mutane sama da 100 a kauyen Tudun Biri a Kaduna, za a hukunta shi. Legit Hausa ya wallafa.
Tinubu ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnati za ta ɗauki ɗawainiyar kula da lafiyar waɗanda suka jikkata a karkashin shirin 'Folako Initiative' wanda za a fara a wannan watan.
A cewarsa, ƙauyen Tudun Biri zai zama gari na farko da gwamnati zata fara ginawa a sabon tsarin da ta ɓullo da shi, kamar yadda Daily Trust ta tattaro.
From ISYAKU.COM