Yan sandan jihar Kano sun cafke kasurgumin dan daba mai suna “Janare” da yan kungiyar sa na fashi da makami su 7


Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Kano sun cafke wani kasurgumin dan daba mai suna Ibrahim Rabiu A.K.A “Janare” da ke jagorantar gungun ‘yan fashi da makami da ke addabar wasu sassan jihar.


 Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Juma’a, 15 ga watan Disamba, 2023, ya ce an kama Janare mai shekaru 27 a Kwanar Ungogo Quarters Kano, tare da wasu ‘yan kungiyar sa guda bakwai.


 A cewar PPRO, an kwato haramtattun kwayoyi, muggan makamai, babura da ba a yi wa rajista ba da dai sauran kayayyaki yayin samamen da jami’an Anti-Daba suka kai.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN