An yi wa mai adaidaita kyautar N100k kan dawo da miliyan 9 a Yobe


An yi wa wani mai adaidaita sahu, Ali Bulama daga kauyen Jumbam, karamar hukumar Tarmuwa da ke jihar Yobe, kyautar kudi N100,000 saboda gaskiyarsa da tsoron Allah.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, matashin mai adaidaita sahun dai ya tsinci kudi naira miliyan 9 sannan ya mayarwa mai shi. Legit Hausa ya wallafa.

Aji Jumbam, mai shekaru 35 ya ce mai kudin, mazaunin Maiduguri ya shiga adaidaitansa a Jumbam da misalin karfe 9:30 na daren ranar 17 ga wata Nuwamba.

Ya ce:

“Da misalin karfe 11:30 ne ko bayan na ajiye shi na koma gida sannan ne na ga wani buhu kunshe da wasu kayayyaki da aka bari a adaidaita sahuna.

“Lokacin da na lura cewa buhun na kunshe da wasu kudade ne, sai na gaggauta fita don neman mai shi. A lokacin, labarin batan naira miliyan 9 din ya rigada ya karade kauyen.

“Bayan dan wani lokaci da taimakon wasu yan kauyen, aka gano mai kudin sannan na mika masa kudin.”

Bulama, wanda ya yo hayar adaidaita sahun, ya ce mai kudin ya ba shi N20,000 a matsayin tukwici.

Shugaban kungiyar sakatarorin dindindin masu ritaya na jihar Yobe, Alhaji Maisandari Lawan, ya gabatarwa Bulama da lambar yabo ta karramawa da kudi N100,000.

Alhaji Lawan ya yaba ma dan adaidaita sahun bisa gaskiyarsa da kuma tsoron Allah.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN