An yanke wa wani mutum hukuncin kisa ta hanyar rataya a Zamfara bisa laifin kashe abokinsa saboda da N100


 Babbar kotun jihar ZamfaraBabbar kotun jihar Zamfara ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga mutum daya da kuma daurin rai-da-rai ga wani a bisa samunsu da laifin kisan kai da yunkurin fashi da makami.


 A yayin shari’ar, mai shari’a Mukhtar Yusha’u, alkalin kotun ya samu mutanen biyu da laifi.


 Anas Dahiru wanda ke zaune a Unguwar Dallatu da ke Gusau a jihar Zamfara, ana zarginsa da daba wa abokinsa, Shamsu Ibrahim wuka har lahira a lokacin da aka samu sabani kan Naira 100 a shekarar 2017.


 Mai shari’a Yusha’u ya samu Dahiru da laifi kuma ya yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya kamar yadda sashe na 221 na kundin Penal code na jihar ya tanada.


 Alkalin kotun ya kuma yankewa Sadiqu Abubakar da laifin yunkurin yin fashi da makami a karamar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara.


 An samu Sadiqu da laifin cin zarafin wani dan kasuwa a kauyen Runji da ke cikin karamar hukumar Bungudu a jihar.


 Mai shari’a Mukhtar Yusha’u ya bayyana cewa Sadiqu Abubakar ya saba sashe na 221 na kundin tsarin tsarin mulki inda aka yanke masa hukuncin daurin rai da rai.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN