Yan Najeriya da dama sun soki Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas kan ware makudan kudade don siyan turare da fanka a gwamnatinsa. Legit Hausa ya wallafa.
Sanwo-Olu ya ware miliyan 7.5 don sauya turaren da ke ofishinsa da kuma biliyan uku na siyan fanka a ofishin mataimakinsa, Hamzat Obafemi.
Sauran sun hada da ware miliyan 440 na siyan motocin alfarma a ofishin shugaban ma'a'ikatansa, cewar Daily Trust.
Har ila yau, ofishin ya samu amincewar miliyan 18 don samar da kaji dubu biyu ga kananan hukumomi da ke jihar da unguwanni.
Gwamnan ya kuma ware miliyan 152 don gyaran ruwa a fadar mai martaba Oba na Legas, Legit ta tattaro.
From ISYAKU.COM