Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a babban birnin tarayya Abuja ta tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Kwamitin alkalan kotun ya tabbatar da hukuncin da kotun zaɓe ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Oluyemi Akintan Osadebay ta yanke wanda ya tsige Abba ranar 20 ga watan Satumba. Legit Hausa ya wallafa.
Idan baku manta ba, Kotun sauraron kararakin zaɓe ta bayyana kuri'u 165,663, daga cikin kuri'un da Gwamna Yusuf ya samu a matsayin haramtatun kuri'u.
Ƙaramar Kotun ta soke waɗan nan kuri'u ne bisa hujjar cewa ba su inganta ba saboda babu satanfi da sa hannun hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) a jikinsu.
Daga nan sai ta rage kuri’un gwamnan zuwa 853,939 yayin da na Nasir Ganuwa, abokin takararsa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ke da kuri'u 890,705.
Bayan haka ne Kotun ta bayyana Gawuna na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan Kano da ƙuri'u mafi rinjaye, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
Gwamna Yusuf ya ki amincewa da hukuncin kotun, wanda ya bayyana a matsayin "rashin adalci," inda ya garzaya kotun daukaka kara.
Da take yanke hukunci ranar Jumu'a, 17 ga watan Nuwamba, 2023, Kotun ɗaukakaka ƙara ta tabbatar da hukuncin da kotun zaɓe ta yanke na tsige Abba.
Ta kuma yanke hukuncin cewa tsaida Abba Kabir Yusuf a matsayin ɗan takarar NNPP ya saɓa wa doka domin bai cancanci ya tsaya takara ba saboda ba ɗan jam'iyya bane.
From ISYAKU.COM