Yan bindiga sun kai sabon hari sun kashe mutane 7 sun sace da dama a Zamfa


Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane bakwai tare da yin garkuwa da wasu da dama a kauyen Gada da ke karamar hukumar Bungudu a jihar Zamfara.

 An tattaro cewa yan bindigan sun kai hari a unguwar da misalin karfe 6:00 na yammacin ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, 2023.

 A cewar mazauna kauyen, ‘yan fashin sun kai farmaki kauyen da ke kan babura da yawa dauke da manyan makamai inda suka fara harbe-harbe kan mutane da dama, inda suka kashe.mutane bakwai.

 A halin da ake ciki, gwamnatin jihar Zamfara ta jajantawa al'ummar Gada bisa harin.

 Mataimakin gwamnan jihar, Mani Malam Muminu, wanda ya kai ziyarar jaje ga iyalan da suka rasa ‘yan uwansu a harin, ya ce wasu mutane takwas sun samu raunuka kuma a halin yanzu suna jinya a asibiti.

 Muminu ya yi addu’ar Allah ya gafarta musu kurakurensu, ya kuma bukaci ‘yan uwa da abokan arziki da su ci gaba da yi musu addu’a da kuma dawo da zaman lafiya a wannan jiha tamu.

 Daga nan sai ya bayar da tabbacin gwamnati na jajircewa wajen daukar nauyin al’amura a karkashin jagorancin maigidan sa Gwamna, Dokta Dauda Lawal Dare na samar da matakan da za su iya kawo karshen ‘yan fashi da sauran miyagun ayyuka a jihar.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN