Wani mutum mai shekaru 34 ya ji rauni bayan ya fado daga silin a lokacin da ya kutsa cikin wani gida a Watsonia, KZN, Afirka ta Kudu.
Reaction Unit Afirka ta Kudu (RUSA) Cibiyar Ayyuka ta Tongaat ta sami kira don taimako daga mai gida bayan ya gano barawon a daya daga cikin dakunan kwana a farkon ranar Litinin, Nuwamba 20, 2023.
Nan take aka tura jami’an suka isa wurin da misalin karfe 07:57.
Mai gidan ya bayyana cewa ya bar gidan ne amma ya koma ya dauko wani abu da ya manta.
Da shiga gidan ya tarar da wanda ake zargin ya kutsa cikin rufin gidan.
Nan take rufin ya ruguje wanda hakan ya sa barawon ya fado ya samu karaya a kafarsa ta dama.
From ISYAKU.COM