Motar Yan sanda dauke da AC CID da Yan sanda 8 ta yi hatsari a Kebbi, sufeto ya mutu

Illustrative picture

Wata mota dauke da jami'an 'yan sanda zuwa wurin aiki wacce ta taso daga hedkwatar 'yan sanda SCID a jihar Kebbi ta samu hatsarin da ya yi sanadin mutuwar wani Sufeto na 'yan sanda.


 A wata sanarwa da Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi SP Nafiu Abubakar ya fitar, ya ce hatsarin ya afku ne a sakamakon fashewar taya. “An samu mummunan hatsarin mota daya tilo a hanyar Koko/Jega, wanda ya hada da motar ‘yan sanda ta Toyota Land Cruiser mai lamba REG. 5465D, dauke da tawagar ‘yan sanda karkashin jagorancin AC CID na rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi, ACP Suleiman Sade da wasu mutane tara.  


A yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa ziyarar wani wurin da aka aikata laifi a kauyen Kendawa, gundumar Dutsinmari a karamar hukumar Koko/Besse. Lokacin da suka isa yankin NNPC a garin Koko, É—aya daga cikin tayoyin motar ya fashe kuma motar ta mirgina sau uku a cikin daji da ke kusa. Nan take tawagar ‘yan sanda daga sashin Koko suka ziyarci inda lamarin ya faru, inda aka kwashe wadanda lamarin ya rutsa da su zuwa Babban Asibitin Koko domin samun kulawa, inda wani Sufeto Sa’idu Idiya na SCID ya mutu kamar yadda wani Likita ya tabbatar.


 Daga bisani an kai gawar tare da sauran wadanda abin ya rutsa da su zuwa FMC da ke Birnin Kebbi domin ci gaba da yi musu magani.


 Allah ya jikan sufeto Sa'id Idiya ya huta a Jannatul Fiddaus, amin.  Tuni dai aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN