Matasa sun kama dan sanda bisa zargin sace kuri'un zabe a Imo, Rundunar yan sanda za ta yi bincike


Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce za ta gudanar da bincike kan zargin tafka magudi a zaben da aka yi wa daya daga cikin jami’anta a jihar Imo.


 Bidiyon wani jami’in da wasu matasa ke rike da shi da suka zarge shi da sace kuri’a a cibiyar tattara kuri’u ta Amakohia Ikeduru a lokacin zaben gwamna da aka yi a ranar 11 ga watan Nuwamba.


 Da yake mayar da martani ga faifan bidiyon, kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya ce;


 ‘’Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta na sane da zargin da ake yi wa wannan dan sanda da ake zargin yana da hannu wajen sace kuri’u a cibiyar tattara kuri’u ta Amakohia Ikeduru da ke jihar Imo.  Ba mu dauki wannan batu da wasa ba domin yana damun sahihancin rundunar da kuma yadda mambobinta za su iya tabbatar da ingancin zabe.  Don haka muna tabbatar wa jama’a cewa za a gudanar da cikakken bincike, kuma za mu yi muku bayani nan da nan.  Yana buĆ™atar cikakken bincike.  Godiya''


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN