Mai sayar da yalo ya yi wa yarinya marainiya yar shekara 9 fyade a Kano kan hanyar dawowa daga makaranta


Wani mai sayar da yalo mai suna Auwalu Abubakar a karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano ya yi wa wata yarinya ‘yar shekara tara fyade.


  Ya aikata laifin ranar 9 ga watan Nuwamba, ya yi sanadin kwantar da yarinyar har mako guda kafin daga bisa a sallame ta daga asibitin ’yan sanda da ke Bompai a birnin Kano.


  Da take zantawa da Daily trust, ‘yar uwar yainyar, Aisha Auwal, ta ce, “An dawo da ita gida tana kuka bayan sun taso daga makaranta;  ta ce ta fada cikin magudanar ruwa.


  “A lokacin da muka nace kuma muka duba ta yadda ya kamata, sai muka gano wandonta na dauke da jini daga al’aurarta.”


  An matsa wa yarinyar domin bayyana wanda yayi mata wannan ajki kafin a garzaya da ita asibitin Murtala Muhammed inda aka tabbatar da anyi mata fyade.


  “Bayan ta bayyana cewa Auwalu, mai sayar da yalo ne, ‘yan sanda sun kama shi,” ta kara da cewa.


  Majiyoyi sun ce yarinyar maraya ce, don haka an yi kira ga hukumomi don tabbatar an hukunta wanda ya aikata laifin.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN