Kotun daukaka kara ta ayyana zaben Zamfara 'Inconclusive', za a sake zabe


Kotun daukaka kara ta raba gardama kan shari’ar zaben gwamna jihar Zamfara. Legit Hausa ya wallafa.


Kotun da ke zamanta a Abuja ta ayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba inda ta umarci sake zabe a kananan hukumomi guda uku.


Kananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da Maradun da Birnin Magaji da kuma karamar hukumar Bukuyun, cewar Daily Trust.


Kotun ta yanke wannan hukunci ne a yau Alhamis 16 ga watan Nuwamba a Abuja inda ta yi fatali da hukuncin karamar kotun a baya.


Har ila yau, kotun ta bayyana cewa kotun sauraran korafe-korafen zabe ta yi kuskure wurin kin yin amfani da shaidun jam’iyyar APC.


Kotun ta kuma yi fatali da sakamakon zaben da jam’iyyar APC da kuma hukumar zabe ta INEC su ka bayar a karamar hukumar Maradun.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN