Kotu ta tsare tsohon gwamnan CBN Godwin Emefiele a gidan yari na Kuje


ban Kotun Tarayya da ke zamanta a birnin tarayya Abuja a Maitama, ta umurci a tsare tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele a gidan gyaran hali na Kuje kafin ya cika ka'idar belinsa.


Mai Shari'a Hamza ne ya bada umurnin a ranar Juma'a bayan gurfanar da Emefiele tare da musanta aikata laifuka shida da Hukumar EFCC ke tuhumarsa a karar da ta yi wa kwaskwarima.


A karar, an zarge shi da amfani da ofishinsa ta hanyar da ba ta dace ba da wasu abubuwan daban, rahoton The Nation.


Mai Shari'a Mu'azu, wanda ya saurari bukatar neman beli da Emefiele ya gabatar, ya dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 22 ga watan Nuwamba don yanke hukunci kan neman belin sannan a fara shari'a ranar 28 ga watan Nuwamba.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN