Hukumar INEC ta bada sanarwar dakatar da zaben sabon gwamna a wasu daga cikin bangarorin jihar Kogi. Legit Hausa ya wallafa.
Hukumar gudanar da zabe mai zaman kan ta watau INEC ta fitar da sanarwa a shafin Twitter a yammacin yau Asabar
Sanarwar ta fito ne daga ofishin Kwamishinan yankin Arewa maso tsakiya wanda ya na cikin kwamitin watsa labarai.
Muhammad Kudu Haruna ya ce hukumar zabe ba za ta karbi sakamakon wuraren da aka samu kuri’un bogi a Kogi ba.
Rahotanni sun nuna lamarin ya auku ne a kananan hukumomin Adavi, Ajaokuta, Ogori/Magongo, Okehi da Okene.
Ko kadan ba za a yarda da wannan ba. Duk sakamakon da bai fito daga hannun hukuma a rumfunan zabe ba, ba zai samu karbuwa ba."
Sanarwar ta ce a sakamakon haka an dakatar da zaben Gwamnan a mazabu tara da ke karamar hukumar Ogori/Magongo da ke Kogi.
Mazabun nan sun hada da Eni, Okibo, Okesi, Ileteju, Aiyeromi. Ragowar kuma su ne Ugugu, Obinoyin, sai kuma Obatgben da Oturu.
Muhammad Haruna ya shaida cewa ana binciken abin da ya faru a sauran kananan hukumomi, kuma za a fitar da matsaya nan da sa’o’i 24.
INEC ta sanar da cewa ba za ta bari ayi magudi a zaben da ake gudanarwa a jihar ba. Dama can Dino Melaye ya yi irin wannan kira.