Jami’an tsaro sun kama shugaban karamar hukumar Igalamela a jihar Kogi, Mista James Onoja a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba.
An kama shi da makudan kudade da alburusai. An cushe kudin da alburusai a cikin jakunkunan ‘Ghana- must-go’ da dama.
An dai yi zargin cewa an yi amfani da kudin ne da alburusai lokacin zaben.
From ISYAKU.COM