Rundunar ‘yan sandan jihar Benue ta kama wata mata mai suna Sughshater Ushahemba, bisa laifin kashe jaririyarta yar watanni 11 da haihuwa a Abeda-Mbadyul a karamar hukumar Logo ta jihar.
Jami’in yada labarai na karamar hukumar Logo, Paul Pevikyaa, ya ce tun farko matar ta yi ikirarin cewa jaririyar nata ta kamu da rashin lafiya da misalin karfe 12:31 na dare kuma ta mutu bayan sa’o’i biyu.
Daga baya ta amsa laifin kashe jaririnta saboda mutumin da ya yi mata ciki ya yasar da ita.
From ISYAKU.COM