Yadda uwargida ta kwada wa maigida dan shekara 67 tabarya a kai ya mutu a Borno


Wata mata ‘yar shekara 40 ta kashe mijinta mai shekaru 67 a garin Banishaik da ke jihar Borno.


 Wani mai sharhi kan harkokin tsaro kuma kwararre kan masu tada kayar baya, Zagazola Makama, wanda ya bayyana hakan ta hanyar X a ranar 22 ga watan Oktoba, 2023, ya ce matar ta kwada wa mijin nata tabarya a kai, wanda ya yi sanadiyar mutuwarsa.


 Har ya zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, babu wani tabbaci a hukumance daga hukumar 'yan sanda dangane da lamarin.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN