Da duminsa: APC ta dakatar da wani shugaba a Jigawa bisa zargin kaura wa yar aikin gidansa cikin gaba da fatiha


Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Jigawa, ta dakatar da shugaban jam’iyyar na karamar hukumar Roni.

 Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban jam'iyar na jihar, Hon.  Aminu Sani Gumel ya fitar.

 An kama Saleh Idris mai shekaru 56 da laifin yiwa ‘yar aikin gidansa fyade.

 A halin da ake ciki kuma, hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya, NSCDC, ta tabbatar da kama Saleh Idris.

 Kakakin hukumar NSCDC reshen jihar Jigawa, CSC Adamu Shehu ya bayyana cewa an kama wanda ake zargin ne a ranar Laraba, 18 ga watan Oktoba, biyo bayan korafin da dan’uwan yarinyar ya kai cewa wanda ake zargin ya yi wa ‘yar uwar sa ‘yar shekara 14 fyade tare da yi mata ciki.  Yarinyar yar aikin gidansa ce.

 “yadda lamarin ya faru shi ne lokacin da wanda ake zargin ya ba ta abin sha a lokacin da matarsa ​​ba ta gida wanda hakan ya sa ta suma kuma ya yi mata fyade.

 “Lokacin da yarinyar ta farfado, sai ya yi mata barazanar cewa kada ta gaya wa kowa ko kuma ta yi kasadar rasa alawus din ta na wata-wata, sakamakon haka, wannan mummunar dabi’a ta ci gaba da maimaituwa ba tare da ta fada wa kowa ba har lokacin da ciki ya bayyana.

 CSC Adamu ya ce da aka yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya musanta zargin kuma an kai karar zuwa kotu.


Latsa NAN don samun Cikakkun LABARAI

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN