Barawo ya sace wa Dan jarida wayar Android a aljihun rigarsa yayin da yake daukar labarai a gidan Gwamnatin jihar Kebbi.
Lamarin ya faru ne ranar Alhamis 5 ga watan Oktoba, lokacin da Dan jaridan ya dukufa wajen daukan jawabin Gwamnan jihar Kebbi da Kamera na gidan Talabijin a gidan Gwamnati bayan hukuncin Kotu.
Tun farko dai an yi umarnin cewa a bari kowa ya shigo gidan Gwamnati kafin jawabin Gwamna, lamari da ake kyautata zaton shi ya ba bata garin dama har suka shigo suka tafka wannan sata duba da cewa Dan Jaridar na tsaye misalin nisan kafa biyar ne kawai daga Mai girma Gwamna Dr. Nasir Idris.
Sai dai bayan tuntubar wani babban jami'in tsaro kan lamarin, ya ce wannan ba sabon abu bane a lamari irin wannan.
Yayin da ake murnar nassara da Gwamna da mataimakinsa suka samu a Kotu, wannan Dan jarida ba zai taba mancewa da wannan rana ba duba da irin ababen amfani da ke cikin wayar na Android.
DAGA ISYAKU.COM