An kuma, Gwamnan Kebbi ya yi alkawarin sake tsago wani muhimmin aiki a garin Birnin Kebbi


Gwamnan jihar Kebbi, Kwamared Dr Nasir Idris Kauran Gwandu ya yi alkawarin gyara garejin Birnin Kebbi (Tashar motoci) domin ganin ya dace da zamani.

 Ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga shugabanni da sauran mambobin kungiyar ma’aikatan sufuri ta kasa (NURTW) yayin da suka ziyarce shi ranar Laraba.

 Gwamna Idris ya bukaci kungiyar ta samar da wurin wucin gadi domin gudanar da ayyukansu na yau da kullum domin dan kwangilar ya fara aikin gyara garejin.

 Da yake yabawa kungiyar ta NURTW bisa irin goyon bayan da gwamnatinsa ke samu daga mambobinta, gwamnan ya bukace su da su ci gaba da gudanar da ayyukansu domin amfanin kungiyar da kuma jihar baki daya.

 Gwamnan ya yi alkawarin samar wa kungiyar motoci a kan lamuni mai sauki wanda za a biya su sannu a hankali, ya kara da cewa rancen ba wai zai bunkasa harkokin kasuwancin su kadai ba, zai kuma kawo musu dauki da ci gaban tattalin arziki.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN