Abun haushi yayin da kato ya bi Malamar addini har ciki dakin ibada ya yi mata fyade


Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta cafke wani mai suna Lekan Sunday bisa zargin yi wa wata Malamar addini fyade a wata coci da ke jihar. Daily trust ta wallafa.

 An ce wanda ake zargin dauke da makami, ya kutsa cikin cocin Orioke Aanu Oluwa Gbohunmi da ke unguwar Ilogbo Adu da ke Kemta a Abeokuta, inda ya yi barazanar kashe Malamar idan ba ta ba shi hadin kai ba, kuma ya sanya wuka a fuskarta.

 Ana zargin Malamar ta fara roĆ™on mai laifin amma ya ki. Daga bisani ya yi mata fyade a cikin cocin.

 Rundunar ‘yan sandan ta kaddamar da farautar wanda ake zargin da ya gudu, bayan ta samu korafi daga Malamar addinin.

 PUNCH ta ruwaito jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Omolola Odutola, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata.

 Odutola ya ce. Malamar addinin ta gane wanda ake zargin mesin ne kuma lebura a yankin.

Ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike yayin da wanda ake zargin yake amsa tambayoyi a wajen Yan sanda. 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN