An gano wakilin Muryar Najeriya, Alhaji Hamisu Danjibga, wanda aka bayyana bacewarsa kwanaki uku da suka gabata, inda aka jefar da gawarsa a cikin sokawe.
Kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) reshen jihar Zamfara, ta yi imanin cewa an kashe shi ne tare da jefa gawarsa a cikin ramin sokawe. PM News ta rahoto.
A wata sanarwa da sakataren NUJ na jihar, Ibrahim Ahmad ya fitar a Gusau ya ce.
“An gano gawar tasa ne sakamakon wani wari mara dadi da yaran makarantar Islamiyya suka shako a bayan gidansa da yammacin Laraba 20 ga Satumba, 2023.
"Bayan an bude sokawe, an tabbatar da gawar Danjibga ne", in ji sanarwar.
An bayyana bacewar Danjibga kwanaki uku da suka gabata kafin a gano gawarsa.
Majiyoyi sun ce da farko an tuntubi iyalansa don su biya Naira miliyan daya domin a sake shi. Sai dai daga bisani sun kara yawan kudin.
Rundunar ‘yan sandan ta cafke mutum daya da ake zargi da hannu a kisan gillar da aka yi wa dan jaridan.
An yi jana’izar marigayin a Gusau kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Published by isyaku.com