Wasu ‘yan ta’adda sun dauki alhakin wani jirgin sama mai saukar ungulu na sa ido na rundunar sojojin saman Najeriya da ya yi hatsari a garin Badna da ke gundumar Chukuba a karamar hukumar Shiroro a jihar Neja.
Rundunar sojin saman Najeriya ta tabbatar da afkuwar hatsarin a ranar Litinin, 14 ga watan Agusta, inda ta kara da cewa sun fara gudanar da bincike don gano musabbabin faruwar lamarin.
Sai dai a wani faifan bidiyo mai tsawon mintuna biyu da dakika goma sha bakwai da suke zagayawa ta yanar gizo, wasu ‘yan ta’adda sun yi ikirarin kakkabo jirgin mai saukar ungulu ta hanyar amfani da bindigar AK47.
Tawagar Daily Trust Fact-Check ta tabbatar da faifan bidiyon wanda suka ce sabon abu ne a yanar gizo kuma yana da damar kasancewa na gaske.
Mai ba da labarin a cikin faifan bidiyon wanda ya yi magana da harshen Hausa, ya ce ‘yan kungiyar Dogo Gide ne, daya daga cikin ’yan fashin da suka addabi sassan jihar Neja, inda suka yi sanadin mutuwar manoma da jami’an tsaro da dama.
Published by isyaku.com