An gano wani jariri dan watanni shida mai suna Chinedu Chukwueke da wata mata ta gudu da shi a garin Minna na jihar Neja.
A baya dai isyaku.com ya bayar da rahoton cewa matar ta sace jaririn ne bayan ta yi yaudarar cewa ita yar koyon aiki ce a shagon gyaran gashi salon na uwar yaron da ke Kure Ultra Modern Market, ranar Lahadi, 23 ga Yuli, 2023.
A wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Twitter a yammacin Laraba, mahaifin jaririn ya bayyana cewa an tsinci jaririn nasa ne a wani juji da ke kusa da ofishin 'yan sanda na Gauraka. Ya ce an samu yaron nasa cikin koshin lafiya.
Published by isyaku.com