Kotun koli ta dage ci gaba da zamanta har zuwa ranar 26 ga watan Mayu domin yanke hukunci kan karar da jam’iyyar PDP ta shigar kan zababben shugaban kasa, Sen. Bola Tinubu da Kassim Shettima, mataimakin shugaban kasa.
Jam’iyyar PDP ta bukaci kotun kolin da ta janye hukuncin kotun daukaka kara, karkashin jagorancin mai shari’a James Abundaga, inda ta ce jam’iyyar ta kasa bada hujjojin dogaro kan karar da suka shigar.
BY isyaku.com
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI