An tsinci gawar wata mata mai suna Maimuna Mohammed Sheke bayan an sace ta daga kauyen Yewuti da ke karamar hukumar Kwali a babban birnin tarayya Abuja.
Wani mai Mai suna Usman Garba Fodio, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce an gano gawarta ne a wani daji da ke karamar hukumar Toto a jihar Nasarawa a ranar Talata, 16 ga Mayu, 2023.
Wani ma’abocin amfani da Facebook, Abdul Jibrin Zubairu Yewuti shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin a wani sako da ya wallafa a Facebook.
"Muna son ki amma Allah ya fi son ki. Ya Maimuna Mohammed sheke, Allah ya sa ranki ya huta lafiya, aljanat firdaus ta zama makomarki ta karshe.
Ku tuna cewa a baya ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu mutanen kauyen 29 a Yewuti.
BY isyaku.com