Wani labari ya bayyana yadda wani mai kula da lambu ya samu ‘yan mata uku ‘yan gida daya ya banka musu ciki.
Tsohon sanatan Najeriya, Shehu Sani ya yada a Facebook cewa, ‘yan matan sun samu ciki ne duk da irin tsaro da killace su da iyayensu ke yi daga shiga mutane. Legit ya ruwaito.
An tattaro cewa, talakan mai kula da lambun shi kadai ne aka ba damar ganin ‘yan matan da kuma kula su a rayuwarsu.
Kamar yadda yazo a rubutun da Sanata Sani ya yada, mai kula da lambun ya fara aikata lalata da ‘yan matan ne ba tare da sanin iyayensu da suka yi zurfi a addinin kirista ba.
Bayan samun labarin abin da ya faru, iyayen sun shiga mamakin yadda lamurra suka sauya duk da irin tsaron da suka sanya a gidansu.
A lokacin da aka tambaye su kan waye ya yi musu ciki, sai suka amsa da cewa mai kula da lambu ne, wanda hakan yasa mahaifiyarsu ta fadi a sume.
Legit.ng ta gano cewa, mai kula da lambun ya fara kulla alakar zina da ta biyu cikin ‘ya’yan ne, wanda daga baya ‘yar fari ta gani abin da ke faruwa bayan kama su hannu dumu-dumu.
Domin neman ta rufa musu asiri, sai ‘yar farin ta nemi mai kula da lambun ya biya mata bukatarta kawai ita ma.
A lokacin da suke aikata alfasharsu, sai ta ukun ta shiga ta kama su hannu dumu-dumu suna aikata lalatar da ta kai ga daukar ciki, ita ma haka ta nemi a biya mata bukata.
Abin da suka aikata dai haka ya kai ga daukar ciki tsakanin ‘yan matan uku, wanda daga baya suka haifi ‘ya’ya
A bangaren iyayen, haka suka daddara suka dauki kaddarar da ta biyo kansu tare da ganin laifin kansu na killace ‘ya’yan nasu.
Duk da an kore shi daga aiki a gidan, har yanzu ‘yan matan na tura masa kudi kana suna kaunarsa a matsayin uban ‘ya’yansu.
Wani mawaki ya ce ya daina dirkawa mata ciki saboda wasu dalilai da ya bayyana a cikin rahotonmu na baya.
BY ISYAKU.COM