An yanke wa wata uwa a Houston hukuncin daurin rai da rai a gidan yari saboda ta yi wa diyarta dukan tsiya har lahira, in ji lauyan gundumar Harris Kim Ogg.
An yanke wa Tradezsha Trenay Bibbs, mai shekaru 29, hukuncin daurin rai da rai a ranar Litinin, 3 ga Afrilu, bayan da aka same ta da laifin kisan kai kan mutuwar diyarta Brielle Robinson mai watanni 4 da haihuwa.
Bibbs ta shaida wa ‘yan sanda cewa ta rika bugun jaririyar a hakarkarinta da kirjinta har sai da ta daina kuka, amma ta kira 911 lokacin da jaririyar ta daina numfashi.
Mataimakin Lauyan gundumar Keaton Forcht ya ce Bibbs ta kashe diyarta saboda mahaifin jaririyar baya son dangantaka da mahaifiyar.
BY ISYAKU.COM
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI