Kayya: An damke wani gurgu da ke sayar da kwaya a cikin keken guragu ba kunya ba tsoro


Wani gurgu da ke amfani da kekensa na guraru wajen sayar da miyagun kwayoyi ya shiga hannun jami’an Hukumar Yaki da Miyagun Kwayoyi (NDLEA). Jaridar Aminiya ta ruwaito.

Kakakin NDLEA na kasa, Femi Babafemi, ya ce an kama gurgun dauke da tabar wiwi mai  nauyin kilo gram 1.3 da kuma lita 10 na kwayar Monkeyy Tail, a samame da hukumar ta kai matattarar masu shaye-shaye a yankin Ekpoma na Karamar Hukumar Esan ta Arewa ta Jihar Edo.

Ya sanar a Abuja ranar Lahadi cewa bayan gurgun, an cafke wata matashiya mai shekaru 19 dauke da miyagun kwayoyi iri-iri da kuma kilo gram 50 na tabar wiwi a boye a yankin Irrua na jihar ana shirin yin fataucinta.

Jami’an NDLEA a Jihar Edo sun kuma cafke wata mata ’yar shekara 46 da lita hudu na Monkey Tail a unguwar Ugbegun da ke Karamar Hukumar Esan ta Tsakiya.

“A Jihar Taraba an kama wani da kwaya 10,009 na tramadol a ranar 17 ga watan Afrilu,” in ji Babafemi.

Hukumar ta kuma cafke wata mace mai shekara 40 dauke da sinki 70 na tabar wiwi a Jihar Imo, da wasu mutum biyu da aka kama da lita 39 na kwayar Skuchies da kuma tramadol da rophynol.

An kuma cafke wani babban dilan kwaya a yankin Okitipup na Jihar Ondo, wanda aka kwace hodar ibis da Heroin da Methamphetamine da Colorado da kuma Loud a hannunsa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN