An kama tsoho mai shekara 70 da ya yi wa yar shekara 4 da yarta mai shekara 7 fyade a watan Azumi


Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa a ranar 4 ga watan Afrilu ta kama wani mutum mai shekaru 70 bisa zargin yi wa wasu kananan yara biyu ‘yan shekara hudu da bakwai fyade a titin Ajiya Jimeta, karamar hukumar Yola ta Arewa a jihar.

 Wanda ake zargin mai suna Usman Ibrahim, an ce ya kai yaran dakinsa da ke kusa da gidan su yaran, inda ya yi lalata da su.

 Mahaifin wadanda abin ya shafa ne ya kai rahoton lamarin ga hedikwatar ‘yan sanda ta Jimeta, bayan ya ga irin radadin da yaran ke ji a lokacin da suke fitsari.

 Binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin mahaifin ‘ya’ya uku ne da ke zaune shi kadai, bayan ya rabu da matarsa ​​shekaru 10 da suka wuce.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje ya tabbatar da faruwar lamarin a takarda da ya raba wa manema labarai.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN