Matar Gwamnan Kebbi Dr Zainab ta share wa Aisha hawaye, bayan zargin ayarin motocin mataimakin Gwamnan Kebbi sun kide mijinta har Lahira wajen aiki a 2019


Uwargidan Gwamnan jihar Kebbi Dr. Zainab shinkafi Bagudu ta tarbi Aisha Attahiru matar sojan da ya mutu a wajen aiki a 2019. Shafin labarai na isyaku.com ya ruwaito.

Ranar Asabar 11 ga watan Maris Aisha ta sami tarbon matar Gwamnan jihar Kebbi a gidan Gwamnati da ke garin Birnin kebbi.

Dr Zainab ta tausaya wa Aisha bisa rasuwar mijinta a wajen aiki. Kuma ta yi mata alkawarin sama mata gida , bayan ta ba ta tallafin injimin nika, deep Fridgzer, kayan abinci da kuma kudi.

Ba ayarin motocin Gwamna Bagudu ne suka kashe mijin Aisha ba.


Bayan Aisha ta kammala yin bayani ga Uwargidan Gwamna, kan abin da ya faru. An fahimci cewa ba ayarin Gwamna Bagudu ne suka kide mijinta ba.

An gano cewar ayarin motocin mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Samaila Yombe ne suka kide L/cpl Attahiru har Lahira a cikin duhun dare a haryar Koko zuwa Yauri.

Lauyan kare hakkin biladama ya jagoranci neman taimako ga Aisha.


Baristar Bashir Umar, Lauyan kare hakkin bi'ladama ne ya jagoranci rubuce-rubuce na neman a taimaka wa Aisha bayan ya Dora daga rubuce-rubuce da wani hafsan soji ya fara tun shekarar 2020.

Barista Bashir ya tabbatar da cewa an aike rubuce-rubucen neman tallafi zuwa ga Gwamnati kafin wannan lokaci.

Hukumar soji ta biya Aisha hakkin mijinta L/cpl Attahiru


Aisha ta tabbatar wa Dr. Zainab Shinkafi Bagudu cewa hukumar sojin Najeriya ta riga ta biya duk hakkokin mijinta.

Kuma tuni ta tashi daga barikin soja zuwa cikin gari domin ci gaba da rayuwa.

Tausayi da Dr Zainab ta nuna


Uwargidan Gwamnan jihar Kebbi Dr Zainab ta nuna hakuri, dattaku, ilimi da jajircewa bisa nuna tausayi ga Aisha da 'ya'yanta biyu.

Dr Zainab ta ce duk da yake mijin Aisha ba ma'aikacin Gwamnatin jihar Kebbi ba ne, Kuma hukumar soji ta biya Aisha hakkinsa. 

An taimaka wa Aisha ne saboda jinkai da kyautatawa amma ba wai tana da wani hakki da ya rataya a wuyan Gwamnatin jihar Kebbi da ya zama wajibi ko dole a aiwatar da shi ba tunda hukumomin soji sun riga sun biya ta hakkin mijinta.

Uwargidan Gwamnan jihar Kebbi Dr Zainab ta taimaka wa Aisha nan take


Daga karshen tattaunawa da aka yi a salo na fahimtar juna, raha dariya da murmushi daga farko har karshesa. Dr Zainab ta tallafa wa Aisha da kyautar deep Fridgzer, injimin nika da kyautar kudi nan take.

Kazalika za a tallafa mata da harkar muhalli nan ba da dadewa ba a cewa Aisha.

Dr Zainab ta shawarci shafin labarai na isyaku.com


Uwargidan Gwamnan jihar Kebbi Dr Zainab Shinkafi Bagudu ta shawarci Malam Isyaku Garba Zuru, Mawallafin shafin labarai na yanar gizo isyaku.com ya yi amfani da shafinsa wajen ciyar da jihar Kebbi gaba.

Ta ce duba da nassarori da shafin isyaku.com ya samu da kuma tasirinsa ga al'umma wajen yada labarai a zamanance. Ta shawarci Malam Isyaku ya ci gaba da kasancewa bangaren nassarorin ci gaban jihar Kebbi.

Latsa nan ka kalli bidiyo

Latsa nan ka kalli Hotuna

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN