Wani mutumi da ya bayyana sunansa Aminu Danmaliki a Facebook ya yi karin haske kan zargin da ake masa cewa ya auri karamar yarinya da bata balaga ba.
Mutumin dan arewa ya ce matarsa ta dara shekaru 21 kuma shi bai auri yarinya yar shekaru 11 ba kamar yadda ake zarginsa. Legit ya rahoto.
Da yake nanata cewar duk zargin da ake masa karya ne, ya bayyana cewa da yardar matar aka yi auren kuma su dukka suna son junansu.
Karanta cikakkiyar sanarwar da ya yi a kasa:
"Aurena na baya-bayan nan da Sakina ya haddasa tashin hankali sosai da kuma zargi mara tushe cewa na auri karamar yarinya da bata balaga ba wasu sun ce shekarunta 11 kuma cewa dole aka yi mata ta aure ni.
Wannan ba gaskiya bane. Bidiyon auren ya yadu. Mun yanke shawarar yin shiru amma aka shawarce ni da na fito na fadi zahirin gaskiya, ga shi nan:
Shekarun matata abun kaunata 21 ita ta zabe ni a matsayin mijinta kuma nima ina sonta. Ina fatan masu bita da kulli da masu shakku za su ga zahirin gaskiya a hoton nan sannan su barmu mu ci amarcinmu."
Masu amfani da soshiyal midiya da dama da suka yi martani ga jawabin nasa sun kuma taya mutumin murnar aurensa sannan suka yi masa fatan samun zaman lafiya.
BY ISYAKU.COM
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI