Type Here to Get Search Results !

Babbar Magana: NDLEA ta kama 'yan kwaya 793 a Arewa, ta kwato miyagun kwayoyi


Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta kama kilo-giram 13,125 na miyagun kwayoyi tare da kama mutum 798 a cikin shekarar 2022. Legit ya wallafa
.

Kwamandan NDLEA a Abuja, Mr. Kabir Tsakuwa ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin da yake magana a taron manema labarai kan illolin miyagun kwayoyi a birnin, Daily Trust ta ruwaito.

Tsakuwa ya bayyana cewa, hukumar ta yi nasara a 2022, inda ya kara da cewa, an kama mutane da kayayyakin bugarwa masu yawa.

Ya kuma shaida cewa, shirin farfado da masu shan kwayoyi na haifar da da mai ido a babban birnin tarayya Abuja.

A cewarsa, an kama jumillar mutane 793 da suka hada da maza 768 da mata 29 a birnin, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Shugaban na NDLEA ya kuma bayyana cewa, an gurfanar da mutum 167 da suka kada da maza 161 da mata shida.

Tsakuwa ya kuma bayyana cewa, an yi nasarar daura mutum 78 da suka hada da maza 74 da mata hudu a kan turba.

Ya kara da cewa, wannan nasara da hukumar ta samu zai rage yawaitar shan miyagun kwayoyi da safararsu a shekarar 2023 da muke ciki.

Hukumar NDLEA ta sha kame masu safarar miyagun kwayoyi da sha a yankuna daban-davan na Najeriya, musamman a shekarar da ta gabata.

An gurfanar da sojan mai shekaru 49, Olanrewaju Lawal, bisa zargin ya shigo da kwayoyin Tramadol da dai sauran haramtattun kayan buguwa.

A lokacin, bayan sauraran batutuwa alkalin kotun ya umarci a ci gaba da ajiye Lawal a magarkama kafin a ci gaba da sauraran kara.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies