Rahotanni da ke zuwa mana yanzu daga kasar Saudiyya shine cewa ba a ga jinjirin watan Ramadana ba a yammacin yau Talata, 21 ga watan Maris. Legit ya wallafa.
Kwamitin neman wata na Hilal karkashin jagorancin Dr. Abdullah Khudairi basu ga watan Ramadana na 1444 ba a yammacin Talata.
Shafin masallacin harami ya rahoto cewa kwamitin wanda ke zaune a Tumair, birnin Riyadh, da sauran yankuna suma basu bayar da rahoton ganin jinjirin watan ba.
Jami’an kotun masarautar sun aika da irin wannan hukuncin zuwa kotun kolin kasar Saudiyya domin sanar da al’ummar kasar da ma duniya labarin sakamakon binciken neman jinjirin watan na yau.
Bayan haka, watan Sha’aban na 1444 zai cika kwanaki 30, sannan watan Ramadan 1444 zai fara a ranar Alhamis, 23 ga watan Maris 2023.
Kamar yadda safin Haramain SHarifain ya wallafa, za a fara sallar Taraweeh a masallatai masu tsarki biyu bayan sallar Ishai daga ranar Laraba, 22 ga watan Maris.
BY ISYAKU.COM
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI