Type Here to Get Search Results !

Zaben 2023: Kano, Kaduna da wasu jihohi 5 na Arewa duk na Tinubu ne, mataimakin shugaban APC

 


Jam’iyyar APC a Arewa maso Yammacin Najeriya ta ce tana da kwarin gwiwar cewa, dan takararta na shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu zai yiwa zaben 25 ga watan Faburairu cin kaja a shiyyar. Legit.ng Hausa ya wallafa.

Arewa maso Yamma ta hada jihohin Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Jigawa, Sokoto da Zamfara, kuma su kadai kuri’u miliyan 22.67 suka mallaka, TheCable ta ruwaito.

A cikin wata sanarwar da Salihu Lukman, mataimakin shugaban APC na kasa (shiyyar Arewa maso Yamma) ya fitar ya ce, yadda gangamin APC ke tafiya da kuma tasirin shugabannin APC nuni NE ga nasarar Tinubu a zaben bana.

Ya bayyana cewa, Tinubu zai samu gagarumin rinjaye a jihohin Arewas maso Yamma saboda karbuwar APC da tasirinta.

Alamu sun nuna APC za ta yi nasara a dukkan matakai, inji Salihu Lukman

A cewarsa:

“Dukkan wadannan alamomi ne na nasara ga APC a Arewa maso Yamma ga dan takararmu na shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a zaben 25 ga watan Faburairun 2023, da ma dukkan ‘yan takara a matakin majalisar kasa.

“Har ila yau alamomin nasara ne ga ‘yan takarar gwamna da majalisun jihohi a dukkan jihohi bakwai na Arewa maso yamma.

“Muna da yakinin cewa da yardar Allah dukkan jihohin bakwai a Arewa maso Yamma, har da Sokoto za su zama jihohin APC a ranar 29 ga watan Mayu."

Ya yi kira ga dukkan mambobin majalisar kamfen na APC a shiyyar da su hada kai da shugannin jam’iyyar a matakai na kasa da sama don tabbatar da nasararta a zaben bana, rahoton BluePrint.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies