Type Here to Get Search Results !

Yanzu-Yanzu: Hadimar Gwamna Tambuwal ta mutu sakamakon cinkoso lokacin kamfen Atiku a Sokoto


Sokoto - Babbar mai baiwa gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, shawara kan ilimin mata, Hajiya Aisha Maina, ta rigamu gidan gaskiya. Legit.ng ya wallafa
.

Hajiya Aisha Maina ta mutu ne yan mintuna bayan halartan taron kamfen dan takarar shugaban kasa jam'iyyar PDP da ya gudana a jihar, rahoton Daily Trust.

An tattaro cewa Hajiya Maina ta shiga cikin wani cinkoso da hargitsi da ya uku a hanyar fita daga cikin filin kwallon Giginya, inda taron ya gudana.

Wata majiya a ma'aikatar labaran jihar wacce ta bukaci a sakaye sunanta tace:

"Wata mai babur ya fadi daga kan babur dinsa yayin da yake kokarin fita daga filin kwallon kuma hakan ya tada hargitsi, mutane suka fara fadawa kan juna. Tana daya daga cikin wanda ta ritsa da su."

Shugaban kwamitin masu baiwa gwamnan shawara, Magaji Gusua shi ma ya tabbatar da aukuwan lamarin inda yace da wuri aka garzaya da ita asibitin koyarwa jami'ar Usmanu Danfodiyo.

A cewarsa:

"Amma abin takaici yan mintuna da kwantar da ita ta mutu."

Magaji ya siffanta ta a matsayin mutum mai kokarin gaske. Ya yi addu'an Allah ya yafe mata kura-kuranta.

Marigayiyar ta kasance tsohuwar shugabar kungiyar mata yan jarida, shiyyar jihar Sokoto.

Tsohon shugaban kungiyar yan jarida NUJ na jihar Sokoto, Isa Abubakar Shuni, ya bayyana kaduwarsa game da mutwar yar jaridar.

Ta bar 'yaya uku.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies