Rikici ya kara tabarbarewa a APC yayin da Aisha Buhari ta tabbatar da ikirarin El-Rufa'i na wasu da ke yi wa Tinubu zagon kasa


Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta tabbatar da kalaman gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai na cewa akwai wasu abubuwa a fadar shugaban kasa dake adawa da takarar shugaban kasa na Bola Tinubu. Legit.ng ya wallafa.

Tinubu, wanda shi ne mai rike da tutar jam’iyyar APC mai mulki, ya ci gaba da nuna bacin ransa kan yawan hare-haren da ake kai masa.

Gwamna El-Rufai a yayin wani shiri kai tsaye ta gidan talabijin a ranar Laraba, 1 ga watan Fabrairu ya zargi wadanda har yanzu ke cikin bakin ciki game da rashin da suka yi bayan tsohon gwamnan jihar Legas ya lashe zaben fidda gwani da laifin kai hare-haren.

Kamar yadda jaridar Nation ta ruwaito, an tattaro cewa Uwargidan shugaban kasa, wacce ta kasance mai goyon bayan Tinubu ce ta dora bidiyon El-Rufai a lokacin da yake yin zarginsa a wani gidan talabijin kai tsaye.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN