Mafita ta samu, CBN ya fadi hukuncin da zai yiwa masu POS da ke karbar sama da N200

 


Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Godwin Emefiele ya ce, dukkan masu hada-hadar kudi na POS da aka kama suna karbar cajin cire kudi sama da N200 za su fuskanci hukuncin jefa su a magarkama. Legit.ng Hausa ya wallafa.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da Najeriya ke ci gaba da fuskantar barazanar karancin sabbin Naira a bankuna da hannun ‘yan POS, Punch ta ruwaito.

Idan baku manta ba, CBN ya nada wakilai daga bankuna da ‘yan POS domin taimakawa wajen musayar kudade a fadin kasar nan.

Da yake magana a ranar Talata yayin da ya ziyarci ministan harkokin wajen kasa, gwamnan CBN ya yi batutuwa kan sabbin ka’idoji da dokokin kudi na CBN.

A cewarsa:

“Lamarin a hankali ya fara lafawa tunda aka kawo tsarin ba da kudi a kan kanta don tagazawa cire kudi ta ATM da kuma a hannun agent-agent dinmu.

“Don haka, babu bukatar sake matsar da wa’adin na ranar 10 ga watan Faburairu.”

Batun umarnin kotu koli

Idan baku manta ba, rahotanni a baya sun bayyana yadda kotun koli ya ba da umarnin a ci gaba da karbar tsoffin kudi har zuwa ranar 15 ga watan Faburairu.

Kotun ya ce, zai sake zama a ranar 15 ga watan domin duba yiwuwar tursasa CBN wajen tabbatar da an ci gaba da karbar tsoffin kudi, rahoton Vanguard.

Har ila yau, Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya shawarci CBN a makon da ya gabata kan ya kara wa’adinsa na 10 ga wata don ba ‘yan Najeriya damar shigar da tsoffin kudi.

IMF ya ba da wannan shawari ne duba da yadda ‘yan Najeriya ke fuskantar kalubalen musayar tsoffin kudade da sabbi a kasar.

Tuni dai ‘yan kasuwa da wasu hukumomin gwamnati a Najeriya suka daina karbar tsoffin kudaden a ranar Litinin saboda bankuna sun daina karbar kudaden.

1 Comments

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

  1. Agaskiya yakamata mutanin dakekan gumnati hattaita gumnati taga tausayin tallakkawa sabeda wannan abin yajifamu chikin yunwa dawahala

    ReplyDelete
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN