KAI TSAYE: Sakamakon zabe a jihar Kebbi, Atiku Abubakar ya lashe kananan hukumomi 9 cikin 10, Aliero ya lashe 7 kawo yanzu


Rahotanni na cewa an karbi sakamakon zaben kananan hukumomi 10 daga cikin 21 da ke fadin jihar Kebbi. Equity FM radio Birnin kebbi ta labarta.

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya lashe kananan hukumomi 9 cikin 10 da aka kammala kirgawa inda dan takarar shugaban kasa na jam'iyar APC Bola Ahmed Tinubu ya lashe karamar hukuma daya.

An kusa kammala kidayar kuri'un dan takarar Sanata na Kebbi ta tsakiya. Yanzu haka an tattara sakamakon kuri'u na kananan hukumomin Gwandu, Aliero, Kalgo, Bunza, Koko Besse, Maiyama, da Jega.

Sai dai har yanzu ana jiran sakamakon karamar hukumar Birnin kebbi. Rahotanni na cewa an sami hakan ne sakamakon batan dabon Jami'in tattara sakamakon zabe na gundumar Marafa da ke karamar hukumar Birnin kebbi. Tare da sakamakon zabe na gunduma ta Marafa.

Wakilin gidan rediyon Equity FM ya rahoto cewa dan takarar Sanata na Kebbi ta tsakiya a jam'iyar PDP Sanata Adamu Aliero, ya sami nassarar lashe zaben kananan hukumomi 7 da aka kammala sakamakon zaben nasu.

Dan takarar Majalisar wakilai na jam'iyar PDP Ibrahim Haliru Muhammad ya lashe sakamakon zabe na kananan hukumomi biyu da aka kammala kirgawa kawo yanzu.

Ku kasance tare da mu don karin bayani......

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN