Jam'iyyar APC ta yi taron masu ruwa da tsaki a Kebbi, duba bin da ya faru


A ranar Larabar da ta gabata ce, masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC reshen jihar Kebbi sun hallara a Birnin Kebbi domin gudanar da wani muhimmin taro don dinke baraka.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya rawaito cewa taron na da nufin tsara dabarun tabbatar da nasara a babban zabe mai zuwa.

NAN ta kuma ruwaito cewa taron ya samu halartar fitattun masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a jihar da suka hada da Gwamna Atiku Bagudu da ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya Alhaji Abubakar Malami.

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da Sen. Bala Ibn Na'Allah (APC- Kebbi ta Kudu), 'yan majalisar wakilai da na jiha, shugabannin jam'iyyar, 'yan majalisar zartarwa ta jiha, dan takarar gwamna na jam'iyyar da dukkan masu rike da tuta a zabe mai zuwa. 

Gwamnan ya ce taron an yi shi ne domin ganawa da kuma yabawa shugabannin jam’iyyar da ‘yan jam’iyyar da kuma al’ummar jihar baki daya.

A cewarsa, an yi yakin neman zabe a ko’ina, kuma kowa na yin iya bakin kokarinsa wajen ganin jam’iyyar ta samu nasara a zabe mai zuwa.

Ya kuma yaba da kokarin kungiyoyin Mata, Campaign Mobilisation na kokarin da ya bayyana a matsayin gagarumin kokarin da suke yi na hada kan mata da goyon bayan jam’iyyar.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN