Type Here to Get Search Results !

Girgizar kasa da aka yi a kasar Siriya da Turkiyya ya yi sanadin mutuwar mutane 2,300

 


Kawo yanzu, rahotanni sun ce yawan wadanda suka mutu a girgizar kasar da ta auku a kasashen Turkiyya da Siriya ranar Litinin sun haura 2,300. Aminiya ta ruwaito.


Girgizar kasar wanda karfinta ya kai 7.8, ta lalata galibin biranen Turkiyya a yankunan da a nan galibin ’yan gudun hijira daga Siriya suke da zama.


Shugaban Cibiyar Kula da Girgizar Kasa na Kasar Siriya, Raed Ahmed, ya ce “Wannan ita girgizar kasa mafi karfin da cibiyar ta taba gani a tarihinta.”


An ga masu aikin ceto na ta kokarin bincike domin gano mutane da kasa ta rufta da su, walau a raye ko a mace.


Akalla mutum 810 aka ce sun mutu Siriya, sannan 1,498 a Turkiyya kamar yadda jami’au suka bayyana.


Kafin wannan lokaci, girgizar kasa mafi muni da Turkiyya ta gani ita ce wadda ta auku a 1939 inda mutum 33,000 suka mutu.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies