Canjin kudi: Ya kamata mahukunta su sake tunani kar tura ta kai bango —JIBWIS

 


Shugaban Majalisar Malamai na Kungiyar JIBWIS reshen Jihar Kaduna, Sheikh Aliyu Abdullahi Telex, ya jawo hankalin mahukunta a Najeriya da su ji tsoron Allah su sake tunani bisa halin da al’umma ke ciki a sanadiyyar sauya fasalin takardun kudi. Aminiya ta ruwaito.

Sheikh Aliyu Telex ya yi wannan kira ne a hudubar Juma’a da ya gabatar a Masallacin Juma’a da ke Tudun Jukun a Zariya.

Ya ce ya zama wajibi su fadakar tare da yin kira ga mahukunta su gaggauta kawo karshen kuncin rayuwa da talakawan Najeriya ke ciki na matsin tattalin arziki da canjin kudi ya jefa su.

Babban Limamin ya kuma gargadi mahukunta da kar son zuciya ya kai su ya baro har hakan ya tunzura al’umma su yi wa gwamnati bore.

Ya ce, duk talaka mai jin yunwa ba abinda ya ke so sai abinci saboda haka ya zama wajibi ga mahukunta a kasar nan su yi wa kansu karatun ta natsu kafin tura ta kai bango.

Sheikh Aliyu Telex ya kuma bayyana cewa karin lokacin canjin kudin da aka yi bai amfani kowa ba saboda babu kudin ma a bankunan.

“Ya mutum da kudinsa amma na hidimar gida ya gagareshi duk da cewa har kwana a kan samu wasu na yi a layin cirar kudi ta na’urar ATM.”

Zan mai da Najeriya cibiyar noma ta Afirka, Tinubu ya shaida wa taron dimbin magoya bayan APC a Kebbi da ba a taba ganin irinsa ba (Hotuna)

3 Comments

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

  1. Wallhi Malam kanfadi gaskiy

    ReplyDelete
  2. Suna son sai sun halaka talaka ne da bakar wahala

    ReplyDelete
  3. Allah ya kara tun farko kowa ya san buhari mugun mutum me dun yayi irin wannan a lokacin mulkinsa na Sojoji a 1983 wallahi mutane da yawa sun mutu lokacin da ya yi irin wannan canji.

    ReplyDelete
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN